BBC navigation

CPC na shirin hadewa da wasu jam'iyyun

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:46 GMT

Taswirar Najeriya

Kwamitin Amintattu na jam'iyyar adawa ta CPC a Najeriya ya amince da shirin jam'iyyar na hadewa da wasu takwarorinta waje guda domin tunkarar jam'iyyar PDP mai mulkin kasar a zabubbukan nan gaba.

Da wannan amincewar, yanzu shugabannin jam'iyyar za su ci gaba da daidaitawa da abokan hadewar tasu, wato jam'iyyar ACN da kuma ANPP game da yadda za su fasalta dunkulewar tasu.

A baya dai jam'iyyar CPC ta yi irin wannan yankuri da wadannan jam'iyyu, amma abin ya ci tura.

Sai dai Sakataren jam'iyyar na kasa,Injiniya Buba Galadima ya shaidawa BBC cewar nan ''Nan ba da dadewa ba za a ji sunayen wadanda zamu nada domin su tabbatarda wannan samun fahimta ko kuma ma dunkulewa baki daya na jam'iyyun adawa a Najeriya''.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.