BBC navigation

Tarayyar Turai za ta baiwa Masar tallafin biliyoyin daloli

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:34 GMT
Shugaba Mohammed Mursi na Masar

Tattalin arzikin Masar ya fuskanci babban koma baya

Kungiyar tarayyar Turai ta amince da wani tallafi na sama da dala biliyan shida da za'a baiwa kasar Masar.

Wata sanarwa data fito daga ofishin shugaba Mohammed Mursi ta ce kudin zai fito ne daga bankin zuba jari na Turai da bankin Turai kan sake gina kasa da ci gaba da kuma wasu kasashe mambobin Tarayyar Turan.

Sanarwar ta zo ne bayan tattaunawar da shugaba Mohammed Mursi ya yi a birnin alkahira tare da shugabar tsare tsaran manufofin kasashen waje ta tarayyar Turai, Catherine Ashton.

Tattalin arzikin Kasar Masar ya gamu da babban koma baya a bangarori da dama, tun lokacin juyin juya halin Kasar da yai sanadiyyar tunbuke Hosni Mubarak daga kan kujerar sa a shekarar 2011

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.