BBC navigation

Mali: AU ta amince da shirin kai dakaru

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:03 GMT

Manyan Hafsoshin sojin kasashen yammacin Afrika suna nazari yadda kwararrun kasa-da-kasa suka tsara yadda sojansu za su kori 'yan tawaye daga arewacin Mali.

Kungiyar Tarayyar Afrika A

U, ta amince da shirin tura sojoji zuwa arewacin Mali domin tumbuke kungiyoyin masu kishin addinin musulunci, wadanda suka kwace iko da yankin a farkon wannan shekarar.

Shugabanin Afrikan na fatan samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya domin suna bukatar taimako ta fuskar kayan aiki da kuma kudade wajen zartar da shirin.

Wannan dai shi ne kudurin da shugabannin nahiyar Afrika za su mika wa kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a kokarin da suke yi na samun iznin majalisar na tarwatsa 'yan tawayen masu kishin Islama dake arewacin Mali din.

Idan dai kwamitin ya amince da shirin, za a tura sojoji fiye da 3000 zuwa cikin katafariyar hamadar arewacin Mali, inda kasashen Najeriya da Nijar da kuma Burkina-Faso ne zasu fi kowace kasar a nahiyar bayar da gudummuwar Soji domin wannan aikin.

Bukatar agajin kayan aiki

Amma kuma wakilin BBC a yammacin Afrika Thomas Fessy ya ce bataliyoyin sojojin na yammacin Afrika zasu bukaci taimakon kayan aiki da kuma na bayanan asiri daga wajen yankin, kazalika da da kuma jiragen saman yaki domin daukar matakin na soji wanda zai iya dauka watanni.

Kungiyar Tarayyar Turai zata tattauna domin duba yiwuwar aikewa da daruruwan masu bayarda horo domin su horarda rundunar sojojin kasar wadda kungiyoyin 'yan tawayen suka galabaitar.

Kwararru kan harkokin tsaro da kuma masu lura da al'amurra sun ce har yanzu za a iya kwashe watanni kafin a shirya rundunarda za ta sake kwato yankin na arewacin Mali.

Hakan kuwa zai samarda karin lokaci domin cigaba da tattaunawar sulhu a bangare daya kasancewar akwai akalla daya daga cikin manyan kungiyoyin mayakan da ta riga ta shiga cikin tattaunawar sulhun.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.