BBC navigation

Obama ya yi karin haske game da murabus din David Petraeus

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:04 GMT
Obama da  David Petraeus

Karin haske game da murabus din David Petraeus

Shugaba Obama ya ce ba shi da shaidar cewa an bada wani bayanin sirri da zai shafi sha'anin tsaron Amurka a abin kunyar da ya kai ga murabus din daraktan hukumar leken asiri ta CIA, David Petraeus.

A jawabinsa ga manema labarai na farko tun bayan sake zabar sa a matsayin shugaban makon jiya, shugaba Obama ya jaddada cewa ana ci gaba da bincike kan abinda ya faru tsakaninsa da wata mace da ba matarsa ba.

Shugaba Obama ya ce tsohon daraktan hukumar ta CIA da ya yi murabus ranar juma'ar da ta gabata ya yi wa Amurka aiki tukuru.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.