BBC navigation

Za a hambarar da shugaban Falasdinawa.

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:31 GMT
shugaban falasdinu Mahmoud Abbas

shugaban falasdinu Mahmoud Abbas

Wasu bayanan sirri na ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila da aka tsegunta wa BBC sun nuna cewa ma'akatar ta bayar da shawarar a hambarar da gwamnatin Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas matukar aka amince da bukatar Falasdinawan ta zama kasa 'yar kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Bayanin ya ce hambarar da Mista Abbas ne kadai mafita idan yunkurin hana faruwar hakan ya ci tura.

Ana sa ran Mista Abbas zai mika bukatarsa ga Majalisar ta Dinkin Duniya ranar 29 ga watan Nuwamba.

Sai dai Isra'ila da Amurka ba su yarda da wannan tsari ba.

Wakilin BBC a kan al'amuran diflomasiyya ya ce wannan barazanar ta Isra'ila wani yunkuri ne na sanya sauran kasashen duniya su ki amincewa da kasancewar Falasdinu a matsayin 'yar kallo a zauren na Majalisar Dinkin Duniya.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.