BBC navigation

Za a amince da dokar haramta auren jinsi daya a Najeriya

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 13:19 GMT

Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Hon. Aminu Waziri Tambuwal

Majalisar wakilan Najeriya ta kammala karatu na biyu kan kudirin dokar haramta aure tsakanin jinsi daya inda baki dayan 'yan majalisar suka yi tir da wannan al'ada, suna cewa ta saba wa koyarwar addini da al'adun al'umomin Najeriya

Wakilin BBC a Majalisar Ibrahim Isa ya ce sabanin yadda aka san 'yan majalisar wakilan Najeriyar da motsa-wuri da kuma murza-gashin-baki a muhawarorinsu, wannan kudirin ya tsallake zangon karatu na biyu cikin ruwan sanyi, saboda babu ko da mutum guda a tsakanin 'yan majalisar da ya nemi ya daga murya da nufin adawa da shi.

Yanzu dai majalisar wakilan ta mika wannan kudiri ga wani kwamiti na musamman don daukar mataki na gaba, ciki har da shirya taron jin ra'ayin jama'a.

Tuni dai da majalisar dattawan kasar ta zartar da dokar haramta auren namiji da namiji ko mace da macen, duk kuwa da wata barazana da wasu gwamnatocin kasashen yamma da kungiyoyi suka yi na dakatar da tallafin da suke baiwa Najeriyar idan har kudirin bai kai labari ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.