BBC navigation

An nada mukaddashin gwamna a jihar Taraba

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:51 GMT
Taswirar Najeriya

An nada mukaddashin gwamna a jihar Taraba

Majalisar Dokokin jihar Taraba ta tabbatar da mataimakin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar a matsayin mukaddashin gwamnan jihar.

Wannan ya biyo bayan wani mummunan hadarin jirgin sama da gwamnan jihar Danbaba Suntai ya yi wanda sanadiyarsa ya samu mummunan rauni

Yanzu haka dai Danbaba Suntai yana kasar Jamus yana jinya.

Tun bayan hadarin ne ake ta takkaddama game da batun nada mataimakin gwamnan a matsayin gwamnan riko domin ya yi aikin gwamna kamar yadda dokokin Najeriya su ka tanadar.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.