BBC navigation

Kamfanin BP zai biya Amurka diyyar dala biliyon hudu

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:07 GMT
bp

Kamfanin mai na BP

Kamfanin mai na British Petroleum wato BP, ya amince ya biya dala biliyan hudu da rabi ga hukumomin Amurka, bisa barnar da ya janyo a yankin tekun Mexico.

Lamarin dai ya janyo malalar danyen mai a cikin teku, shekaru biyu da suka wuce.

A karkashin 'yarjejeniyar da ya yi da ma'aikatar shari'a ta Amurka, kamfanin na British Petroleum-BP ya ce zai amsa laifufuka 14 , ya kuma biya diyyar dala biliyan daya da dubu dari uku.

Bugu da kari kuma ya biya wasu karin dala biliyan uku ga wasu kungiyoyi a Amurka.

Da ma dai kamfanin ya British Petroleum-BP ya fara biyan diyya ga wasu jama'a da masana'antu da kuma ma'aikatun gwamnati, abun da ya sa illahirin diyyar da zai biya ta tashi a dala biliyan arba'in.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.