BBC navigation

An fadakar da musulmi muhimancin yin amfani da kalandar muslunci

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:48 GMT
Saudi Arabia

Shekarar musulunci ta tsaya

A Jamhuriyar Nijar, wasu kungiyoyin addinin muslunci sun gudanar da wani babban taro a birnin yamai domin fadakar da al'ummar a kan muhimancin yin amfani da kalandar muslunci a tsakanin musulmi.

Sun yi taron-ne saboda shigar sabuwar shekarar musulunci a yau, wato shekarar 1434 bayan hijira

Malaman da su ka halarci taron na ganin yana da mahimmacin gaske musulmi su rike kuma su rinka amfani da Kalandar musulunci, a madadin riko da al'adun nasara

Malaman sun bayyana cewa rashin sanin Kalandar kan haifar da rigingimu musamman a lokacin soma azumin watan Ramadana

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.