BBC navigation

China ta bayyana sababbin shugabanninta

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:56 GMT

Shugaban China mai jiran gado XI Jinping yana jagorantar sauran mukarrabansa zuwa wajen taro da manema labarai.

Jam'iyyar Communist mai mulkin Kasar China ta bayyana sababbin shugabannin da za su shugabanci kasar a tsawon shekaru goma masu zuwa.

Wasu wakillan Jam'iyar ta Communist ne da aka zazzabo suka zabi 'yan kwamitin dindindin mai wakilai bakwai da ake kira Politburo wadanda sune za su kasance Shugabannin zartarwa na kasar.

Kamar yadda aka yi tsammani mataimakin shugaban kasar Xi Jinping, shi ne ya gaji shugaba mai barin gado, Hu Jintao a matsayin shugaban Jam'iyya kuma shugaban kasa.

An kuma nada mataimakin Premier LI Keqing a zaman mutum na biyu a mukami a kwamitin kuma wanda zai rike mukamin Firaministan kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.