BBC navigation

'Ana cin zarafin kananan 'yan mata a Morocco'

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:52 GMT
Kungiyar kare hakkin dan Adam

Ana sa kananan 'yan mata aiki a Morocco

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch dake da Hedikwatar ta a birnin New York na Amurka, ta ce ana cin zarafin 'yan mata da ke barance a Morocco, kuma wasun su, shekarun su ba su ma zarta 8 ba.

Kungiyar ta ce dubban irin wadannan 'yan mata na aiki na tsawon sa'o'i 12 a rana, ba tare da sun samu hutu koda na rana guda ba, kuma albashin da ake ba su bai wuce dala 10 ba a wata.

Har ila yau Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce ana yiwa 'yan matan duka da sanda ko da bututun roba.

Kakakin kungiyar Human Rights Watch Jo Becker ta ce Kusan dukkanin 'yan matan su na aiki ne ba bisa ka'ida ba, saboda dokokin kwadago na Morocco sun haramta daukan 'yan mata ko duk wasu yara 'yan kasa da shekaru 15, aiki.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.