BBC navigation

Masar ta yi Allah-wadai da Isra'ila

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:04 GMT

Muhammad Morsi, shugaban kasar Masar

Shugaban Masar, Muhammad Mursi, ya yi Allah Waddai da hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza, kuma tuni ya maido da Jakadan Masar a Isra'ilar, gida.

Mr Mursi ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda Isra'ilan ta kashe a Gaza, yana mai bayyana su da cewa shahiddai ne.

Ya ce matakin da Isra'ila ta dauka, zai yi zagon kasa ga zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha, Alexander Lukashevich ya ce Irsa'ila tana amfani da karfi fiye da kima a hare-haren da take kaiwa zirin Gaza.

Ya yi kira ga Palasdinawa masu fafutika da su dakatar da harba makaman roka a cikin Isra'ila, yana mai cewa kisan fararen hula daga duka bangarorin 2, abu ne da ba zaa laminta da shi ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.