BBC navigation

An kai harin ramuwar gayya da roka cikin Isra'ila

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:04 GMT
Rikicin Israela da Palasdinawa

Rikicin Isra'ila da Palasdinawa na kazancewa

An jin Karar jiniyar wani farmaki na sama da aka kai a birnin Tel Aviv na Israila a karo na farko cikin shekaru 20, a yayinda rokokin da 'yan bindigar Palasdinawa su ka harba ke sauka kusa da garin

Ba a dai samu labarin jikkata ba daga rokokin biyu, wadanda suka sauka a kudancin birnin da kuma tekun Mediterenean

Sai dai hare haren akan birnin na Tel Aviv- wanda keda nisan fiye da kilomita saba'iin da arewacin Gaza, na nuna yadda fadan ya rinchabe a ranar laraba, a lokacin da Isra'ila ta hallaka komandan Kungiyar Palasdinawa ta Hamas

Fira ministan Masar Hisham Qandil zai kai ziyara a Gaza

An shirya Fira ministan Masar, Hisham Qandil zai kai ziyara a Gaza a gobe Jumaa.

A fahimtar BBC dai, gwamnatin Masar na fadi tashi don shiga tsakani a rikicin da ke faruwa yanzu haka tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.

Tuni dai shugaban Masar din Muhammad Mursi, ya yi Allah Wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza, yana mai cewa matakin zai yi zagon kasa ga zaman lafiya a yankin.

Kasar ta Masar dai ta bude wurin tsallaka iyakarta na Rafah, domin karbar Palasdinawan da suka samu raunika.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.