BBC navigation

'Ya kamata Najeriya ta rage dogaro a kan mai'

An sabunta: 15 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
oil

Matatar danyen mai

A Najeriya, hukumar dake kula da rabon arzikin kasar wato Revenue Mobilization Commission a turance, ta yi gargadin cewa lokaci ya yi daya kamata gwamnatin Tarayya dana jihohi su maida hankali wajen fadada kafofin samun kudin shigarsu maimaikon dogaro da mai.

Hukumar ta ce mai fa na iya karewa, saboda haka bai kamata a saki-jiki sai ya kare ba.

Mafi yawan jihohi a Najeriyar dai sun dogara ne da kason da suke samu daga gwamnatin tarayya, lamarin da hukumar ke cewa nada hadarin gaske.

Wannan matakin da gwamnatin keyi ya janyo an daina maida hankali a kan ayyukan noma da kuma sarrafa albarkatun kasa.

Kwararru sun sha nanata cewar idan aka cigaba da irin wannan kasar za ta iya shiga wani irin yanayi idan danyen mai ya kare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.