BBC navigation

Amurka ta yi kira a matsa lamba kan Hamas

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:14 GMT

Barack Obama

Amurka ta yi kira ga kasashen Masar da Turkiyya da wasu kasashen Turai su matsa lamba a kan kungiyar Hamas ta kawo karshen harin rokoki a kan Isra'ila.

Fadar gwamnatin Amurka White House ta ce ta ji takaicin rayukan farar hula da aka rasa a Gaza, to amma wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurkar Mark Toner ya ce alhakin kawo karshen rikicin yana kan kungiyar Hamas.

Mark Toner ya kara da cewa, "Isra'ila tana da 'yancin kare kan ta."

Prime Ministan kasar Masar Hisham Qandil zai kai ziyara yau Jumma'a zuwa garin na Gaza - to amma kasar ta Masar ta ce manufar ziyarar don ta nuna goyon bayan ta ne ga al'ummar Palasdinawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.