BBC navigation

CIA ta fara bincike kan murabus din Petraeus

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:21 GMT

David Petraeus

Hukumar leken asiri a Amurka, CIA ta ce ta fara wani binciken sakamakon murabus din da Janar David Petraeus Daraktan Hukumar ya yi a makon da ya gabata sakamakon laifin da aka same shi da aikatawa na neman mata alhali kuma yana da aure.

Wani mai magana da yawun Hukumar CIA ya ce za a yi binciken ne da nufin gano wasu bayanai kuma hukumar na fatan za ta koyi wasu darussa daga binciken.

David Petraeus din ya yi murabus ne bayan ya amsa cewar yana neman wata ma'aikaciyar sa Paula Broadwell.

A ranar Litinin, hukumar bincike ta tarayyar Amurka FBI ta kwashe na'urori masu kwakwalwa daga gidan ta, tana mai cewar ta mallaki wasu muhimman bayanai.

Amma Janar Petraus din ya ce, bai taba gaya mata ko kuma ba ta irin wadannan bayanan ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.