BBC navigation

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:08 GMT

Hari a Gaza

An shafe daren jiya ana kai harin bama-bamai a Gaza a yayinda Isra'ila ta kara azama a hare-haren da take kai wa Kungiyar Hamas.

Wani wakilin BBC a Gaza ya ba da rahoton cewar da safiyar yau ma an kai harin da wasu manyan bama-bamai.

Isra'ila ta ce cikin kasa da sa'a daya a jiya Alhamis, ta kai hari a kan wasu na'urori fiye da saba'in na harba makaman roka da aka girke a karkashin kasa.

Mayakan na Palasdinawa sun cigaba da harba rokokin jefi-jefi a kan biranen Isra'ila da suka hada da Tel Aviv.

Tun lokacin da harin da Isra'ila ta kai birnin Gaza da yayi sanadiyyar mutuwar wani Kwamandan mayakan Hamas da kuma wasu fararan hula goma sha takwas rikicin ya kara kazanta tsakanin Isra'ila da kuma Hamas.

Sanarwar da Gwamnatin Isra'ila ta bayar na fitar da sojojin shirin ko ta kwana dubu talatin na nuni da tabbacin rade radin da ake yi cewa Isra'ilar za ta kai harin kasa zuwa Gaza.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.