BBC navigation

Qandil ya yi Allah-wadai da hare-haren Isra'ila a Gaza

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:41 GMT
Hisham Qandil da Muhammed Mursi

Masar ta yi allawadai da hare haren Isra'ila

Firayim Ministan Masar, Hisham Qandil, ya yi Allah-wadai da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza, wadanda ya ce mummunan bala'i ne.

Ya bayyana haka ne a wata 'yar gajeriyar ziyara da ya kai a yankin.

Ministan Masar, Hisham Qandil dai ya shafe kasa da sa'o'i uku ne a ziyarar sa zuwa zirin Gaza.

Ya bayyana harin da Isra'ila ta kai a Gazan a matsayin babban bala'i da kasashen duniya ya kamata ta dauki mataki a kai.

Mista Qandil kuma ya ziyarci daya daga cikin manyan asibitocin dake zirin gazan, inda aka kai gawar wani mutumi da kuma wani yaro dan shekaru biyu da suka rasu sakamakon harin da Israila ta kai.

Bangarorin biyu dai na zargin juna da saba alkawarin tsagaita wuta da aka cimma a baya.

Israila dai ta shafe daren jiya tana luguden wuta ta sama, inda sojojinta suka ce sun kai hare hare a wajaje kusan 150.

A dai dai lokacin da Mista Qandil din ke wannan gajeruwar ziyarar a Gaza dai, an samu hare hare ta sama da kuma fashewar abubuwa inda hayaki ya turnuke sararin samaniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.