BBC navigation

Mun kashe wanda ya kashe Janar Shuwa —JTF

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:20 GMT
Ola Ibrahim

Babban Hafsan Dakarun Tsaron Najeriya, Admiral Ola Ibrahim

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani jagoran kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad—wacce aka fi sani da suna Boko Haram—wanda ya bayar da umarnin kisan wani tsohon janar na soja da aka yi kwanan nan yayin wani "babban hari" ranar Alhamis.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: "Yayin harin da kuma mayar da martani, dakarunmu sun kashe wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram a yankunan arewa maso yamma da arewa gabas, Ibn Saleh Ibrahim, da mukarrabansa".

Sanarwar ta kara da cewa "an tabbatar da cewa marigayi Ibn Saleh ne ke da alhakin kisan jarumin nan na lokacin Yakin Basasa, marigayi Janar Mamman Shuwa, a bisa umarnin jagoran kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau".

Ranar 2 ga watan Nuwamba ne dai wadansu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kashe Janar Shuwa a kofar gidansa da ke birnin Maiduguri.

Sanarwar ta rundunar sojin Najeriya ta ci gaba da cewa za ta ci gaba da kai hari, kuma tuni ta samu nasarar gano wadansu makamai da abubuwa masu fashewa.

Kakakin Rundunar Tsaro ta Hadin Gwiwa mai aikin tabbatar da tsaro a Jihar Borno, wato JTF, Laftanar Kanar Sagir Musa, ya ce an yi amfani da jirage masu saukar ungulu da motoci masu sulke wajen kai harin.

Sai dai kuma ya ce bai san adadin mutanen da aka kashe yayin harin ba.

Sagir Musa ya kuma ce sun kama makamai da dama a samamen da suka kai.

A lokuta da dama sojojin Najeriya kan bayyana irin nasarar da suka samu wajen yaki da wadanda suka kira 'yan ta'adda, amma ana zargin suna boye adadin sojojinsu da aka kashe ko kuma fararen hular da suka rasa rayukansu a lokacin harin.

Rahotanni daga Maidugurin na cewa wadansu mazauna wasu unguwannin da aka kai samamen a jiya sun kauracewa gidajensu don gudun abin da zai biyo baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.