BBC navigation

Ana yunkurin sasantawa da wakilan mayakan Islama na Mali

An sabunta: 16 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:33 GMT
Blaise Compaore

Shugaba Blaise Compaore na Burkina Faso

Shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Compaore, na wani kokarin sasantawa tsakanin wasu daga cikin kungiyoyin masu kaifin kishin Islama da 'yan tawayen Abzinawa na kasar Mali da su ka kwace arewacin kasar bayan juyin mulkin da aka yi a watan Maris.

Ya ce yana tattaunawa ne da kungiyoyi biyu—wato Ansar Dine da kungiyar MNLA.

Ana wannan tattaunawa ne a daidai lokacin da kasashen Afirka ta Yamma ke shirin tura dakaru kasar ta Mali, domin yakar tawaye a arewacin kasar.

Tarayyar Afrika da Faransa, kasar da ta yiwa Malin mulkin mallaka, sun yi kira da a sasanta.

Najeriya dai ta ce za ta tura dakaru zuwa Malin a cikin makwanni masu zuwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.