BBC navigation

Saliyo na yin zaben Shugaban kasa

An sabunta: 17 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:15 GMT

Tutar Saliyo

A yau Asabar, jama'ar kasar Saliyo ke kada kuri'un su a zaben Shugaban kasa da majalisar dokoki.

Shugaban kasar mai ci yanzu Ernest Koroma, yana neman wani wa'adin mulki ne karo na biyu a wani abin da ake hasashen za ayi fafatawa ta kut-da-kut da babban abokin hamayyar sa tsohon Shugaban mulkin sojin kasar Julius Maada Bao.

Zaben dai wata alama ce ta baya-bayan nan na farfadowar kasar Saliyo daga mummunan yakin basasar da aka dade ana gwabzawa wanda ya kawo karshensa shekaru goma da suka gabata.

Shugaba Koroma ya jagoranci shirin farfado da tattalin arzikin kasar cikin hanzari, abin da masu sukar lamirin sa suka ce yana tattare da mummunan cin hanci da rashawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.