BBC navigation

Gaza: Ana neman tsagaita wuta

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:24 GMT

Wata tawagar Isra'ila ta isa birnin Alkahira na Masar yayinda ake cigaba da kokarin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Kai tsaye dai jami'an gwamnatin Isra'ila sun shiga tattaunawa da jami'an gwamnatin Masar.

Wani dan kungiyar Palasdinawa ta Hamas ya ce tattaunawar da ake yi ta maida hankali ne akan samar da ka'aidojin tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Babban sharadi

Sai dai Ministan Harkokin Wajen Isra'ilar, Avigdor Lieberman, ya ce sharadin farko na sasantawa shine dole Paledinawa su daina harba rokoki daga Gaza zuwa Isra'ila.

Ya ce: "Ba wai Isra'ila ba kawai, ba bu wata kasar da za ta amince da abinda zai sanya fiye da mutanenta milyan daya su shige su boye; kuma fiye da wasu milyan dayan ba su iya gudanar da harkokinsu na yau-da-kullum.

"Ba su zuwa makaranta, ba su zuwa aiki. Yaa zama cewa karar jiniyar kai hari da kuma hare-haren rokoki ne ke juya halin rayuwarsu,"" inji shi.

'Yan gwagwarmaya na Palesdinawa dai sun ci gaba da harba rokokinsu.

Amma Isra'ila ta ce ta harbo guda biyu a yau, wadanda suka tsinkayi birnin Jerusalem.

Isra'ilar ma na ci gaba da kai hare-haren, wadanda kungiyar Hamas ta ce sun jawo halakar mutane sittin da bakwai a kwanaki biyar da aka shafe ana kaisu.

Mai magana da yawun gwamnatin Paledinawa, Nour Odeh, ta ce 'yan jarida ma basu tsira daga hare-haren Isra'ila ba.

Ta ce: "Isra'ila ta kaiwa 'yan jarida Palesdinawa hare-hare dari ukku.

"A shekarun baya munyi asarar abokan aikinmu 20 saboda mamaye yankin Palsdinawa da Isra'ilar ta yi.

"Yau kuma sakon adawa da 'yancin yada labarai da bayyana ra'ayin jama'a a bayyane yake," inji ta.

A wani harin da Isra'ilar ta kaima wani jami'in Hamas dai, an kashe mutane tara 'yan gida daya.

An samu rudani a Asibitin Shifa dake Gaza yayinda likitoci ke kokarin kula da wadanda harin Isra'ila ya jikkita.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.