BBC navigation

Netanyahu ya ce za'a fadada hari ga Gaza

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:06 GMT

Piraministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce a shirye yake ya fadada kai farmaki akan 'yan kungiyar Hamas dake yankin Gaza sosai saboda ci gaba da harba rokoki cikin Isra'ila da su ke yi.

Yanzu dai an shiga rana ta biyar a hare-haren da Isra'ila ta ke kaiwa a yankin Gaza.

Jami'an kiwon lafiya na Palasdinawa sun ce daya daga cikin hare-haren na Isra'ila ya hallaka wasu yara kanana su biyu, 'yan gida daya.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Hamas ta ce ya zuwa yanzu Isra'ila ta hallaka akalla mutane fiye da hamsin, kuma rabinsu fararen hula ne.

Sai dai kuma Isra'ilan ta ce ta dan bude mashigar yankin Gaza domin bada damar shigar da kayan agaji.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.