BBC navigation

'Yan tawayen Congo sun koma kai hare-hare

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:44 GMT

'Yan tawayen M23 a Congo

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna matukar bacin ran sa ga matakin da 'yan tawaye suka dauka na sake komawa kai hare-haren da suke yi a gabashin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

Lokacin da ya yi wata ganawar gaggawa, kwamitin sulhun ya yi kira ga kungiyar 'yan tawaye ta M23 ta gaggauta dakatar da dannawar da take yi zuwa Goma babban birnin lardin.

A ranar asabar, 'yan tawayen suka kwaci garin Kibumba duk da ruwan bama-baman da kananan jigaren yakin Majalisar Dinkin Duniya ke yi masu.

Kwamitin sulhun kuma ya yi kira da a daina nuna goyon baya ga 'yan tawaye daga wasu kasashen ketare.

Jami'an kasar Congo sun ce 'yan tawayen na samun goyon baya daga kasar Rwanda, zargin da Rwandar ta musanta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.