BBC navigation

Akwai alamun tsagaita wuta a Gaza-Morsi

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:33 GMT

Shugaban Masar Mohammed Morsi

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya ce akwai alamun nan ba da jimawa ba za a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Palasdinawa a Gaza.

Sai dai kuma ba shi da wani tabbaci a kan haka,ya kuma gargadi Isra'iala ta guji kaddamar da hari ta kasa a kan gaza.

Yace, "idan aka yi mamaya ta kasa kamar yadda aka ambato wani Jami'i a Isra'ila na cewa, zai haddasa mummunan sakamako ga yankin baki-daya.

Mr Morsi yana magana ne bayan tattaunawar da yayi a birnin Alkahira a game da rikicin na Gaza da Prime Ministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Isra'ila ta musanta rahotannin da aka bayar cewa ta tura wakilan ta wajen tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira.

Shugabannin kungiyar hada kan Larabawa Arab league dake yin taro a birnin Alkahira sun nuna goyon bayan su ga kokarin da kasar Masar ke yi na shiga tsakani.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.