BBC navigation

'Yan tawaye a Syria sun kwace filin jirgin sama

An sabunta: 18 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:38 GMT

'Yan tawayen Syria

'Yan tawaye a kasar Syria sun ce sun kwace wani filin jirgin sama da sojojin gwamnatin Syriyar ke amfani da shi a sakamakon wani mummunan fada da suka gwabza a dab da kan iyakar Iraqi.

Masu fafutukar suka ce an kashe mayakan 'yan tawayen goma sha-biyu lokacin da sojojin Shugaba Assad suka mayar da martani ta hanyar jefa manyan bama-bamai kan filin jirgin saman a Dera al-zour mai arzikin man fetur.

Magoya bayan 'yan adawa sun ce an kashe sama da mutane dubu talatin da shida tun lokacin da aka fara rikicin a cikin watan Maris na bara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.