BBC navigation

'Yan tawayen Colombia sun ce za su tsagaita bude wuta

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:46 GMT
Ivan Marquez, wakilin FARC a tattaunawar

Ivan Marquez, wakilin FARC a tattaunawar

Kungiyar 'yan tawayen Colombia ta FARC ta yi shelar tsagaita bude wuta ta kashin kai na tsawon watanni biyu, bayan da ta fara tattaunawar sulhu ta gaba da gaba da gwamnati, a karon farko cikin shekaru goma.

Bangarorin biyu na ganawa ne a kasar Cuba, domin lalubo hanyar warware rikicin da aka shafe kusan shekaru hamsin ana fama da shi.

Gwamnatin Colombiar ba ta mayar da martani ba tukuna.

Sai dai duk da haka, babban wakilinta a wurin shawarwarin, Humberto de la Calle, a jiya Lahadi, ya jaddada cewar rundunar sojan kasar za ta ci gaba da yakar 'yan tawayen har zuwa lokacin da zasu rattaba hannu akan yarjejeniyar karshe ta amincewa su ajiye makamansu.

Ya yi watsi da kiraye kirayen da kungiyar FARC ta yi a baya na a tsagaita wuta, yana mai cewar hakan zai ba 'yan tawayen wata dama ce kawai ta kara tara makamai da kuma jan damara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.