BBC navigation

'Yan tawayen Congo na dannawa Goma

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:11 GMT

Jamhuriyyar Dimkoradiyyar Congo

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dake gabashin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun ce al'amura na kara cabewa a yayinda dubban mutane ke tserewa daga yankin saboda dannawar da 'yan tawaye ke yi zuwa birnin Goma.

A yanzu dai tazarar da ta rage wa 'yan tawayen na kungiyar M23 kadan ce tsakaninsu da Goma babban birnin lardin duk kuwa da ruwan bama-baman da suke sha daga kananan jiragen yaki na Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan tawayen sun ce ba su da wani shiri na kwace birnin, to amma mazauna birnin na fargabar cewa nan ba da jimawa ba zai fada hannun su.

Rahotanni sun ce wasu rundunonin sojin Congo dake kare garin na Goma sun arce sun bar wuraren da suka ja daga.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.