BBC navigation

'Yan tawayen M23 na neman sulhu

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:38 GMT
Dakarun 'yan tawaye na M23

Dakarun 'yan tawaye na M23

'Yan tawaye a gabashin jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun baiwa gwamnatin kasar wa'adin sa'o'i ashirin da hudu na ta bude kafar tattaunawar sulhu, kuma ta janye dakarunta daga garin Goma, hedkwatar yankin.

Gwamnatin Congo ta ce ba zata tattauna da 'yan tawayen kungiyar M23 ba, sai dai da Rwanda kadai, wadda ake zargi da mara baya ga 'yan tawayen.

Dubban mutane ne ke ta tattara ina su ina su suna tserewa yayinda 'yan tawayen ke kara dannawa gaba. 'Yan tawayen sun ce a yanzu sun dakata kilomitoci kadan tsakaninsu da garin na Goma.

'Yan tawayen sun cigaba da nausawa zuwa wani yanki da bai fi kilomita kalilan daga garin Goma babban birnin kasar ba.

'Yan tawayen na M23 sun ce ba su da shirin kwace iko da garin, sai dai mazauna yankin suna tsoro saboda kada nan gaba 'yan tawayen su karbe garin.

A karshen makon da ya gabata ne kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi alwadai da hare-haren da 'yan tawayen ke kaiwa, tare da bukatar a kawo karshen tallafin da 'yan tawayen ke samu daga kasashen waje, ganin cewa a yanzu suna dauke ne da muggan makamai.

Ministan harkokin wajen birtaniya William Hague ya soki cigaba da nausawar da 'yan tawayen na M23 ke yi, tare da bukatar 'yan asalin birtaniya da ke zaune a Goma su bar garin.

Har yanzu dai dakarun gwamnati da na majalisar dinkin duniya ne ke cigaba da iko da filin tashi da saukar jiragen sama dake Goma, sai dai majalisar dinkin duniya ta ce halin da al'ummar garin ke ciki ya tsananta yayinda mutane dubu 60 suka gudu suka bar gidajen su.

A ranar asabar din data gabata 'yan tawayen sun kwace garin Kibumba dake da nisan kilomita 30 daga arewacin Goma, suna kuma dab da shiga arewacin gundumar Kivu wadda ke kusa da iyakar kasashen Rwanda da Uganda.

Majalisar dinkin duniya ta ce dakarun wanzar da zaman lafiyarta sun gwabza da 'yan tawayen a ranar lahadin data gabata inda suka yi amfani da makaman Roka da kuma kai harbi ta sama a jirage masu saukar ungulu.

Wakilin faransa a majalisar dinkin duniya Gerard Araud ya lura cewa ba za a samu sasanta rikicin ba, har sai an samu yarjejeniya tsakanin Jamhuriyar demokradiyyar Congo da makwabtan ta ciki har da Rwanda.

Sai dai Ruwanda ta musanta zargin da ake cewa 'yan tawayen na samun goyon bayan dakarunta ta hanyar basu makamai.

Sai dai kuma kwararru a Majalisar dinkin duniya sun ce suna da shaidar da ke nuni da cewa 'yan tawayen na samun goyon bayan Rwanda, inda aka kuma bukaci kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniyar da ya sanyawa manyan jami'an Rwanda takunkumi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.