BBC navigation

Wadanda suka mutu a Gaza sun kai 80- Hukumar Lafiya

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:45 GMT

Hare-haren Israila a Gaza

Hukumomin lafiya a Gaza sun ce adadin mutanen da aka kashe a ruwan bama-baman da Isra'ila ke cigaba da yi a Gaza ya karu zuwa tamanin.

Jiya lahadi, ita ce rana mafi muni tun lokacin da aka fara rikicin kwanaki biyar da suka wuce.

A wani hari guda ya yi mummunan ta'adi an kashe mutane goma sha-daya 'yan gida daya lokacin da Isra'ilar ta jefa wani bam a kan gidan wani jami'in kungiyar Hamas.

An cigaba da kai harin bama-baman a tsawon daren jiya, wani bam din ya tarwatsa Hedikwatar 'yan sandan Hamas.

A na su bangaren kuma Palasdinawan sun cigaba da harba rokoki zuwa Isra'ila, to amma har yanzu ba a sake ba da rahoton mutuwar wasu mutane ba tun ukun nan da aka fada a ranar Alhamis.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.