BBC navigation

Sojoji sun yi ta duka da kama jama'a a garin Garissa na Kenya

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:57 GMT
Garin Garissa

Garin Garissa

Sojoji masu dama a garin Garissa na arewa maso gabashin Kenya sun bazama kan tituna suna ta duka, suna kuma kama mutane, bayan da aka bindige har lahira uku daga cikin dakarunsu a yau Litinin.

Wani dan jarida a garin ya ce sojojin sun kutsa kai cikin wani masallaci, inda suka fatattaki masallata.

An bindige sojojin uku har lahira, wadanda kuma dakarun rundunar kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika ne, lokacin da suka tsaya domin gyara motar su da ta lalace.

An dora laifin hare- hare makamantan wannan a garin a kan 'yan kungiyar al-Shabaab ta Somalia.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.