BBC navigation

Reuters ta fitar da Video kan yadda sojan Najeriya ya kashe wani

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:34 GMT

Ola Ibrahim Shugaban Rundunar Sojin Najeriya

Kamfanin Dillancin labarai na Reuters ya fitar da wani hoton Video wanda ya nuna wani Sojan Najeriya yana bindige wani mutum da sojojin suka kama.

Hoton Videon - wanda BBC bata tabbatar da shi ba, ya nuna wani mutum yana rokon a yi masa rai, to amma, aka bindige shi har lahira a gaban gawarwakin wasu mutane da dama da aka kashe.

Rundunar Sojan Najeriyar ta musanta hoton videon a matsayin na boge - tana cewar babu yadda za a yi sojojin Najeriyar su yi wannan aika-aika.

A can baya dai an zargi sojojin Najeriyar da laifin kashe mutane ba tare da wata shari'a ba a yakin da suke yi da kungiyar nan ta Boko Haram.

Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya ce wani soja ne ya ba da hoton videon wanda ya ce ya na wurin lokacin da aka aikata kisan makonni biyu da suka gabata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.