BBC navigation

Shugaba Obama na Amurka na ziyara a Burma

An sabunta: 19 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:15 GMT
Barack Obama a Burma

Shugaba Barack Obama na Amurka a Burma

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi kira ga hukumomin Burma da su kara bullowa, tare da aiwatar da sauye-sauye a kasar, a lokacin wata gajeriyar ziyara da ya kai, wadda ita ce ta farko da wani shugaban Amurka ya kai can.

Cincirindon jama'a ne suka yi masa marhabin yayin da ake zagayawa da shi a cikin birnin Rangoon, inda kuma ya gana da shugaban kasar, Thein Sein, da kuma jagorar 'yan adawa, Aung San Suu Kyi.

Shugaba Obama ya yaba da sauye-sauyen da ake aiwatarwa ya zuwa yanzu, ya kuma yi alkawarin Amurka za ta ci gaba da taimakawa.

Sai dai ya ce babu wata hujja ta barkewar tashin hankali tsakanin Musulmi da mabiya addinin Buddha a yammacin kasar ta Burma.

A cewarsa, "Babu wata nasara da za a samu wajen aiwatar da sauye-sauye matukar ba a sasanta tsakanin al'ummar kasa ba".

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.