BBC navigation

'Yan tawaye sun kwace Goma'

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:53 GMT

Dakarun 'yan tawaye a gabacin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo sun ce sun kwace garin Goma.

Yanzu haka akwai dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya akan titunan garin amma dai ba su da yawa kuma ba ruwansu da 'yan tawayen.

A jiya gwamnatin Congon ta yi watsi da sharuddan da kungiyar yan tawayen ta gabatar na tattaunawar sulhu.

Congon na zargin Rwanda ne da marawa 'yan tawayen na M23 baya -- zargin da Rwandar ta musanta.

Tunda farko dai masu aiko da rahotanni sun ce sun ga wata runduna ta sojojin 'yan tawayen su na tinkarar titin dake tsakiyar birnin tare da tinkarar wajen da sojojin Congo suke, inda duka bangarorin biyu suka bude wa juna wuta.

An yi ta jin karar harbe-harbe a cikin garin Goma tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawayen.

Kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo, Laftanal Janar Chandar Prakash, ya ce 'yan tawayen sun yi kokari kai wa dakarunsa hari tun daga filin jiragen sama na kasar amma hakan ya ci tura.

Ya kara da cewa 'yan tawayen sun fake ta bayan gidajen fararen hula wajen kaucewa dakarun Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan ya ba su damar shiga cikin garin.

Garin Goma dai na da muhimmanci sosai ganin cewa ya na kan iyaka ne tsakanin kasashen Rwandan da Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Gari ne na kasuwanci da ke da ababen more rayuwa da kuma sansanin sojojin Majalisar Dinkin Duniya.

Saboda kusancin da garin yake da shi da Rwanda ana samun 'yan kasuwar da ke tsallakowa domin cinikin ma'adanai.

Yawan 'yan kasuwar Goma da su ka fito daga kasar Rwanda ya sanya ana yi masa kallon tamkar a kasar garin yake maimakon a kasar Congo.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.