BBC navigation

An kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:14 GMT
Sojojin Isra'ila

Sojojin Isra'ila

Wasu majiyoyi na Palasdinawa masu dama na cewa za a bada sanarwar cinma tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila cikin sa'o'i masu zuwa, duk da Isra'ila na cewa ba ta kammala daddalewa ba kan kulla wata yarjejeniya.

Majiyoyin kungiyar Hamas na cewa akwai yuwuwar a fara aiki da yarjejeniyar da karfe sha biyun dare agogon can, duk da cewa wasu jami'an Palasdinawa da na Masar na nuna cewa ana dab da cinma tsagaita wuta, amma ba a riga an karkare ba.

Gwamnatin kasar Masar na aiki tukuru dan ganin an kawo karshen zub da jinin da ake yi a Israela da Gaza a kwanakin da suka gabata, da safiyar yau ne shugaban Masar Muhammad Morsi ya ce yana sa ran za a dakatar da rikicin cikin sa'o'i masu zuwa.

Tun a wancan lokacin jami'an Masar da manyan mambobin kungiyar Hamas suka ce an daidaita, kuma ana sa ran za a sanar da hakan a yammacin yau.

Sai dai wani jami'in Israela ya shaidawa BBC cewa sojoji za su cigaba da ayyukansu har sai an dakatar da harba makaman rokar da ake harbawa Israela daga Gaza.

Yayin da a bangare daya mai magana da yawun gwamnatin Israela ya ce ba a cimma matsaya ba akan batun.

A yanzu Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Mr Ban Ki Moon ya tattuna da prime ministan Israela Benyamin Natanyaho a Jerusalam, bayan da ya kwashe kusan rabin yini a alkahira babban birnin kasar Masar.

Mr Ban Ki Moon ya gargadi Isarela da kar ta yi kutse ta kasa a Gaza domin tuni hare-haren da take kaiwa ta sama suka janyo mutuwar fararen hula dama kuma hakan ba a bin a amince da shi ba ne.

Haka nan ana sa ran sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton za ta isa yankin nan ba da jimawa ba.

Sai dai rahotannin da ke fitowa daga yankin na nuni da cewa, Israela ta watsa wasu takardu ga mazauna wasu yankunan Gaza da su fice, kuma masu aiko da rahotannin sun ce tuni wasu iyalan suka fara ficewa.

An kuma ci gaba da kai hare hare tsakanin bangarorin biyu yayinda ake ci gaba da dakon ayyan tsagaita wuta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.