BBC navigation

Ana taron inganta wutar lantarki a Najeriya

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:28 GMT

A Nageriya an bude wani taron yini daya akan yadda za a inganta harkokin samar da wutar lantarki a kasar.

Taron dai ya tattaro wakilan kasashen Yammacin Africa da Turai da Amurka kan yadda zasu bayar da gudunmowarsu akan inganta harkokin samar da wutar lantarki a kasar.

Gwamnatin Najeriya dai na kokarin shigar da 'yan kasuwa a harkar samar da wutar lantarkin, wanda ta ce ta haka ne kadai za'a samu isashshiyar wutar lantarkin da kasar ke bukata.

Rashin ingantacciyar wutar lantarki dai na jawowa Najeriya asarar biliyoyin daloli ta fuskar masu saka hannayen jari a kasar.

Yanzu haka kasar Afrika ta Kudu, wadda ba ta da yawan mutanan da Najeriya ke da su, ta na samar da sama da megawatt 40,000 yayinda Nageriyar ke samar da megawatt 4,000 kawai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.