BBC navigation

Mali: Amurka ta yi tayin bayar da taimakon soji

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:28 GMT

Mayaka masu kishin Islama a kusa da filin jirgin saman birnin Gao a arewacin Mali.

Kasar Amurka ta ce tana sa ran kasashen Yammacin Afrika zasu bukaci taimakonta dangane da shirin aikewa da sojoji zuwa arewacin Mali don sake kwato yankin daga hannun 'yan tawaye.

Wani kwamandan rundunar sojin Amurkan dake sa ido kan harkokin Afrika, Janar Carter Ham ya shaidawa BBC cewa koda yake kawo yanzu ba a gabatar da bukatar neman taimakon ga Amurka ba a hukumance, yana sa ran za a bukaci hakan a fannin bada horo da samar da kayyakin aiki tare da jigilar dakarun da za a tura zuwa yankin.

Wannan furuci na Amurkan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa mayaka 'yan kishin Islama sun fatattaki 'yan tawayen Abzinawa daga garin Menaka a arewacin Malin.

Kungiyar Tarrayyar Afrika dai na jiran iznin Majalisar Dinkin Duniya ne domin tura sojojin taron dangi dubu uku zuwa yankin da manufar kwato shi daga hannun mayaka masu kishin addinin Musulunci wadanda suka karbe iko da shi tun a farkon wannan shekara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.