BBC navigation

Har yanzu Dangote ne yafi arziki a Afrika

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 17:27 GMT
dangote

Alhaji Aliko Dangote

Attajiri dan Najeriya mai kasuwancin siminti, Alhaji Aliko Dangote, mai shekaru hamsin da biyar da haihuwa, ya ci gaba da kasancewa mutumin da yafi kowa arziki a Afrika, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana a jerin attajirai 40 na nahiyar.

Ya ci gaba da jagorantar sauran masu kudi a nahiyar Afrika, inda arzikinsa ya kai dala biliyan 12, fiye fa dala biliyan 10 da yake dasu a bara.

Daga cikin jerin masu arzikin su 40, akwai wasu mutane uku da suka samu shiga jerin a karon farko, wato daya daga Najeriya da kuma wasu biyu daga Afrika ta Kudu.

Sani Bello wanda a yanzu dukiyarsa ta kai dala miliyon 425, yana harkoki ne na mai da kuma sadarwa. Kamfaninsa na AMNI Petroleum nada rijayar mai na cikin teku, sannan kuma yana da kaso a kamfanin sadarwa na MTN Nigeria.

A karon farko an samu mata biyu a cikin jerin masu arziki 40 a Afrika wato Folorunsho Alakija ta Najeriya da kuma Isabel dos Santos diyar tsohon shugaban kasar Angola.

Sunayen masu arziki goma da yawan arzikinsu:

1. Aliko Dangote $12, 000 55
2. Nicky Oppenheimer da iyalansa $6, 400 67
3. Johann Repert da iyalansa $5, 700 62
4. Nassef Sawiris $5, 500 51
5. Mike Adenuga $4, 600 59
6. Christoffel Wiese $3, 700 71
7. Othman Benjelloun $2, 750 80
8. Patrice Motsepe $2,650 50
9. Naguib Sawiris $2, 500 58
10. Mohammed Mansour $2, 200 64

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.