BBC navigation

An kwana ana ruwan bama-bamai a Gaza

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:22 GMT

Yadda Jirage yakin Isra'ila ke kai hari cikin dare akan birnin Gaza

Sojoji Isra'ila sun kwashe daren jiya Talata suna cigaba da luguden wuta kan Zirin Gaza, a daidai lokacin da aka kasa kai karshe ga batun shirin tsagaita wuta.

Makamai masu linzami da Isra'ila ta harba sun lalata wani ginin gwamnatin Hamas da ke tsakiya birnin.

Sai dai su ma Falasdinawa sun cigaba da mayarda martani da harba rokoki sama da 150 kan yankunan Isra'ila a jiya kawai; abinda yayi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa.

A cikin sa'oin da suka wuce hare-haren na Isra'ila sun kara kamari inda a jiya talata kawai aka kashe Falasdinawa akalla ashirin.

Sakon gargadi

An kuma cigaba da jin karar fashewar bama-bamai a cikin birnin na Gaza wanda yawancinsa ke cikin duhu saboda lalacewar na'urorin wutar lantarki.

Kafin hakan dai jiragen yakin Isra'ilan sun watso wasu takardun akan zirin na Gaza masu dauke da sakonnin da ke gargadin mazauna wasu yankunan zirin dasu kaura zuwa tsakiyar birnin Gaza kuma su bi wasu kebantattun hanyoyi.

Takardun dai na cewa ne ''ba ku ne soja ke kaiwa hari kuma ba su son cuta muku da iyalanku''.

Sai dai Hamas ta bukacin Falasdinawa da su yi biris da sakon wanda ta kira dabarar yaki ta hanyar yaudara.

Ko da yake Israila tayi da'awar yiwa mayakan Hamas mummunan ta'adi da kai hare-haren jiragen sama kimanin 1550 a cikin mako dayan da ya wuce, hare-haren sun kasa dakatarda hare-haren rokokin da mayakan Falasdinawa ke kaima ta.

Fiye da makaman roka 1,400 ne aka harba mata ciki harda kusan 200 da aka harba jiya talata wadanda suka hallaka Isra'ilawa biyu cikinsu har da soja daya.

Biranen Qudus da Askalan na daga cikin wureren da Falasdinawan suka kai ma hari.

A daren Talata ma 'yan sanda Isra'ila sun ce wani makamin roka da Falasdinawa suka harbo ya fada kan wani gida a birnin Rishion Lezion inda ya raunata mutane biyu kuma ya lalata gidan.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacinda Kasashen Masar, Amurka, da kuma Majalisar Dinkin Duniya ke cigaba da kokarin diplomasiya na shiga tsakani a rikicin.

Farayin Ministan Isra'ilar Benyamin Natanyahu ya ce ya fi son ganin an samu magance rikicin ta diplomasiya idan hakan zai yiwu.

Yace ''yanzu dai idan akwai yiwuwar samun magance wannan matsalar ta hanyar diplomasiyya da zai dauki lokaci mai tsawo mun fi son hakan. In kuma babu, na tabbata kun fahimci cewar Isra'ila zat a dauki duk wani matakin da ya wajaba domin kare al'ummarta.''

Sai dai Wani kakakin Hamas Osama Hamdan ya shaidawa BBC cewar rokokin da suke harbawa ne ke tilastawa Israi'a maganar yin sulhu:''Muna wannan ne domin nuna wa Isra'ila cewar Falasdinawa na iya kare kansu kuma ga shi yanzu suna maganar a yi sulhu.''

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.