BBC navigation

Harin Mumbai: An zartar da hukuncin kisa kan Ajmal

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:27 GMT

Hotel din Taj dake birnin Mumbai inda aka kai harin

An rataye dan bindiga daya tilo da ya rage a raye cikin wadanda suka kaiwa birnin Mumbai na kasar Indiya hare-hare a shekara ta 2008, inda suka kashe mutane mutane sama da 160.

An dai rataye Muhammad Ajmal Kassab dan kasar Pakistan ne da safiyar laraba a kurkukun Yerwada dake jahar Maharashtra a yammacin kasar ta Indiya.

Rahotanni sun ce an zartarmasa da hukuncin na kisa ne da misalin karfe bakwai da rabi na safe agogon kasar ta Indiya watau karfe 2.00 na dare agogon GMT bayan da shugaban kasar Prenab Mukherjee ya ki amincewa da rokon afuwar da ya yi a farkon wannan watan.

Ministan harkokin cikin gida na Indiya Sushil Kumar Shinde ya shaidawa manema labarai cewar ofishin jakadancin kasar da ke Pakistan ya shaidawa gwamnatin kasar ta Pakistan game da shirin rataye Ajmal Kassab din.

Tuntubar diflomasiya

Shinde ya kara da cewar kuma Indiya a shirye take ta mikawa Paskistan din gawarsa idan ta bukaci hakan.

Sai dai ya ce ya zuwa yanzu babu wata bukatar hakan daga Pakistan.

A watan Agusta ne dai Kotun Kolin kasar Indiya ta tabbatar da hukuncin kisan da wata kotun ta yanke masa a baya sakamakon samunsa da hannu a jerin hare-haren da aka kaiwa birnin Mumbai na kasar ta Indiya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 166, amma ya daukakka kara.

Muhammad Ajmal Kassab dai dan kasar Pakistan ne ke cikin kungiyar nan mayaka da ake kira Laskar-e-Taiba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.