BBC navigation

Rikici: an kama mutane 200 a Taraba

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:53 GMT

Hukumomi a Jihar Taraba dake arewa maso gabacin Najeriya sun ce sun kama kimanin mutane 200 da suke zargi da hannu a tashin hankalin da aka yi a garin Ibi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma kone-konen kadarori a wannan makon.

Hukumomin dai sun ce sun kama mutanen ne da makamai daban daban kuma suna kan bincike da nufin gurfanar da su gaban kotu yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da sintiri a yankin.

To amma mazauna garin na Ibi na kokawa da dokar hana zirga-zirga da aka kafa masu.

Tun bayan barkewar rikicin ne dai hukumomin Najeriya suka tura karin dakarun tsaro domin maido da doka da oda a yankin.

Hukumomin sun ce sun kama dimbin mutane masu dauke da muggan makamai, wadada suke zargi da hannu a tashin hankalin mai nasaba da addini da kabilanci.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba, Amos Olaoye, ya ce: "Mun kama mutane 200 da ake zargi a yankin na Ibi, wasunsu kuma an kama su ne dauke da makamai da suka hada da bindigogi kirar gida, da adduna da dai sauran makamai.

"Har yanzu muna bincike, ba mu gabatar da su a kotu ba tukunan. Da zarar mun kammala bincike za mu gabatar da jerin zarge-zarge da kuma tuhumce-tuhumce da suka dace.

"Haka kuma da zarar mun kammala bincike, zamu sanar da jama'a ko tabbas mutane na da hannu a rikicin ko kuma a'a.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa dukkan mutanen da aka kama na can tsare a hedikwatarta dake Jalingo, babban birnin jihar ta Taraba.

Rundunar ta musanta rahotanni dake cewa dakarun tsaro sun yi musayar wuta da mutanen kafin su ka kama su.

Kwanaki kalilan bayan rigimar, yanzu kura ta lafa, amma jama'ar yankin na ci gaba kokawa da dokar hana fita ba dare ba rana da mahukunta suka kafa a yankin.

A tashin hankalin da aka yi a ranakun Lahadi da Litinin na wannan mako dai rahotanni sun ce an kashe mutane kimanin goma ne, amma hukumomi a nasu bangaren na cewa mutane biyu ne aka kashe.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.