BBC navigation

''Mu muke aika wa Hamas da makaman roka''- Iran

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:24 GMT

Hossain Sheikhulislam, wakili a kwamitin taimakawa gwagwarmayar Falasdinawa na Iran

A yayinda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila ta kankama, wani jami'in gwamnatin Iran ya ce kasar ta aikewa Hamas da makaman masu yawa a yayin fadan da ta kwashe kwanakki 8 tana gwabzawa da Isra'ila.

Hussain Sheikhullislam, wanda mashawarci ne ga kakakin majalisar dokokin kasar kuma wakili a kwamitin tallafawa gwagwarmayar Falasdinawa a Iran, ya ce ko baya ga haka, sun kuma baiwa Falasdinawan horo.

'' Ya kamata mu sumbaci hannayen wadanda suka aike da rokoki zuwa can. Ya kamata mu yi la'akari da wahalar aikewa da manyan makaman roka da bindigogin harba su da kuma bayar da horo a Zirin Gaza- inda mutun ba zai iya aikewa da ko da gwangwani daya na madarar jarirai ba. Aiki ne wurjanjan, ya kamata mu taya al'ummar Iran Murna''. Inji jam'in a cikin wata hira da gidan tallabijin na kasar.

A lokacin fadan dai wanda ya lakume rayukan Falasdinawa 155 da kuma Isra'ilawa 5, Israila ta kai hare-hare ta jiragen sama sau 1550 yayin da Hamas ta harba mata rokoki akalla dubu daya.

Musantawa

Sai dai kuma wani rahoton da kamfanin dillacin labaran Iran din na Mehr ya buga wani rahoto dake cewar kwamandan rundunar juyin-juye halin kasar Birgediya Janar Ja'afari ya musanta cewar Iran ta aike da wani makami kai tsaye zuwa Gaza.

Yace Iran ta dai baiwa faladinawa fasahar kera su ne kawai.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.