BBC navigation

Gaza: Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa Mursi

An sabunta: 22 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:15 GMT

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wata sanarwa wadda a cikinta yake kira ga Isra'ila da Hamas da su kiyaye yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a Alkhahira.

Kwamitin ya yabawa Shugaban Masar Muhammad Mursi da wasu saboda rawar da suka taka wajen shiga tsakani, inda kuma ya yi kiran a kaiwa Gaza agajin gaggawa.

wakiliyar BBC a hedikwatar Majalisar ta Dinkin Duniyar Nada Tawfik ta ce wannan shi ne sako na farko da ya fito daga Kwamitin Tsaron tun farawar tashin hankalin.

Wakilan Kwamitin dai sun kasa yin kiran a kawo karshen zubar da jini tun farko ne bayan da Amurka ta ki amincewa da fitar da wata sanarwa ranar Talata wadda ba ta bayyana Hamas a zaman ummul-khaba'isun kazantar rikicin ba.

Zaman lafiya mai tangal-tangal

Wannan sanarwar da aka fitar ranar Laraba dai ba ta dora wa kowane bangare laifi ba, amma ta yi kira ga duka bangarorin biyu da su yi da gaske wajen aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar.

Kwamitni ya kuma nanata muhimmancin samar da cikakken zaman lafiya ta hanyar baiwa Falasdinawar damar kafa kasar kansu.

Shi ma Babban Sakataren Majalisar ta dinkin duniya Ban-ki-Moon ya nanata irin wannan kiran. A jawabin da ya yi wa wakilan kwamitin ta naurar bidiyo daga birnin Tel Aviv, ya ce halin da ake ciki a yankin ba wanda ke iya dorewa ba ne kuma akwai bukatar yin jan aiki wajen samarda dakatar da wuta mai karko.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.