BBC navigation

An kammala taron kasashen D8

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:56 GMT

Shugaban Pakistan Asif ali Zardari

Shugabannin Kungiyar kasashe takwas masu tasowa da ke da yawan al'ummar Musulmi da ake kira D8 sun kammala taron kolin kungiyar wanda aka gudanar a Pakistan.

Kasashen da ke kungiyar dai sun hada da Bangladesh, da Indonesia, da Iran, da Malaysia, da Masar, da Najeriya, da Pakistan, da kuma Turkiyya.

Shugabannin dai sun mayarda hankali ne a kan bunkasa alakar cinikayya da zuba jari a tsakanin kasashensu.

Najeriya dai za ta karbi bakuncin tattaunawar bunkasa cinikayyar tsakanin kasashen na D8 wadda za a yi a watan Febrairu mai zuwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.