BBC navigation

Ana tarzomar siyasa a kasar Masar

An sabunta: 23 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:41 GMT

Muhammed Mursi, shugaban Masar

Masu adawa da shugaba Muhammad Mursi na kasar Masar sun cinna wuta ga ofisoshin jam'iyyar 'yan uwa musulmi mai mulkin kasar a birane da dama.

Wasu masu zanga-zangar kuma sun yi maci domin nuna goyon baya ga shugaban bayan da bayyana kudurin dokar da ya bashi iko kan komai-da-komai a kasar, yana mai cewa na wucin gadi ne, kuma ana kokarin kare manufofin juyin-juya halin da aka yi a kasar ne wanda ya kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Sai dai kungiyoyin masu sassaucin ra'ayin addini sun yi zargin cewa kudurin wani sabon mataki ne na mulkin kama-karya. Banbancin ra'ayi tsakanin masu kishin addini da masu sassauci na kawo tsaiko ga yunkurin rubuta sabon tsarin mulkin kasar.

Sa'o i kadan da fitar da sabin dokoki, masu zanga zanga suka fito kan tituna a birnin Alkahira da ma sauran wasu birane.

Suna zargin cewa shugaba Morsi na neman zama mai kama karya kamar mutum da ya gada a karagar mulki, shujgaba Hosni Mubarak.

Su ma dai magoya bayan shugaban kasar sun taru a kofar gine ginen gwamnati a birnin Alkahira, suna cewar karfin ikon da ya kara ma kansa zai kasance na wucin gadi ne.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.