BBC navigation

An yi babban taro kan 'yan tawayan Congo

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:14 GMT
'Yan tawayen gabashin Congo

'Yan tawayen gabashin Congo

Shugabannin kasashen Afurka sun yi kira ga 'yan tawaye a gabashin janhuriyar Demokradiyya Congo da su dakatar da hare haran da suke kaiwa.

A karshen wani babban taro da su kai yau a Kampala babban birnin kasar Uganda, shugabannin sun yi kira ga 'yan tawayen M23 da su janye daga garin Goma wanda suka kwace kwanannan.

Har ila yau shugabannin sun yi kira ga shugaban kasar Congo, Joseph Kabila, da ya duba korafe korafan 'yan tawayan.

Shugabannin kasashen Afurka hudu ne suka halacci taron---- to amma shugaban kasar Rwanda, Poul Kagame, ya kaurace masa.

Ana zargin Rwanda da goyan bayan 'yan tawayan M23 din---- zargin da ta musanta.

Yan tawayan dai sun sake dannawa zuwa wasu yankunan dake hannun gwamnati bayan da suka kwace iko da garin Goma.

Shima shugaban 'yan tawayen na farar hula ya halartar taron, amma ba'a tabbatar ko a wane matsayi ya je wajan wannan babban taron koli na kasashen yankin Great Lakes a gabashin Afurka ba.

'Yan tawayen dai sun nemi tattaunawar sulhu gaba ga daba tare da gwamnatin Kinshasa.

Sai dai kuma shugaban kasar janhuriyar Demokradiyyar Congo, Joseph Kabila, ya ce shi zai sasanta ne kawai da gwamnatin Rwanda.

A halin da ake ciki dai 'yan tawayen sun ci gaba da nausawa ta bangaran kudanci da arewaci daga garain Goma inda suka fi karfi.

Majalisar dinkin duniya ta ce dakarunta dake kasa za su yi kokarin hana 'yan tawayen ci gaba da nausawa wuraran da suka sa gaba, sai dai ta ce dakarun wanzar da zaman lafiyar ba za su yi abin da za su maye gurbin sojojin gwamnatin Congon ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.