BBC navigation

Alkalai a Masar na adawa da matakin Morsi

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:24 GMT
'Yan adawar Masar

'Yan adawar Masar

Manyan alkalan kasar Masar sun kalubalanci matakin da shugaban kasar, Muhammad Morsi ya dauka na baiwa kansa gagarumin iko.

Kuma suka ce, matakin da shugaban kasar ya dauka wata babbar barazana ce ga zaman cin gashin kai na bangaren shari'ar kasar.

Alkalan sun fitar da sanarwar ce kwana guda bayan zanga-zangar nuna rashin amincewa da matakin da shugaban kasar ya dauka.

Wannan wata muhimmiyar sanarwa ce da dama akai tsammaninta daga bangaran shari'a, kungiyar dake wakiltar manyan alkalan kasar ta Masar.

Inda suka ce wannan wani yunkuri ne na raunata bangaran shari'a a kasar, kuma sun ce sun yi kira ga shugaba Morsi da ya koma tsarin da ake a da.

Alkalan suna duba yiwuwar tafiya yajin aiki.

A baya lokacin da shugaban kasar ya yi kokarin korar babban mai shigar da kara na kasar an tilastamasa fasawa.

A wannan karan yana iya tunkaho da yabon da ya samu daga kasashen duniya na shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiyar da akai a kan Gaza, ko da yake Amurka ta soki batun karawa kansa ikon da ya yi.

Yanzu haka 'yan kalila daga cikin tantunan masu zanga zangane suka rage a dandalin Tahrir, kuma an yi kiran da a fito wata zanga zangar nan gaba a yau.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.