BBC navigation

Mohamed Morsi na Masar ya yi jawabi kan bore

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:38 GMT

Zanga-zanga a Masar

Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya yi wani jawabi ga magoya bayansa da suka hallara a Fadar sa dake birnin Alkahira...inda ya yi alwashin kare juyin-juya hali na kasar da kuma jan ragamar kasar ta Masar ga samun 'yanci da dimokradiyya.

Ya ce, "Ina so in shaida muku da kuke a nan da sauran jama'a, magoya baya na da masu adawa da ni, ni bai dame ni ba da nake da 'yan adawa, sabanin haka ma ina fatan ace akwai masu adawar ta gaskiya."

Kungiyoyin 'yan adawa sun zarge shi da laifin nuna halayyar masu mulkin kama-karya bayan da ya baiwa kansa sababbin jerin iko a ranar Alhamis.

Masu bore daga kungiyoyin 'yan adawa sama da ashirin sun yi zaman dirshan a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.