BBC navigation

Paparoma ya kaddamar da manyan limamai

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 22:02 GMT

Paparoma Benedict ya kaddamar da wasu manyan malaman cocin Roman Katolika masu matsayin 'Cardinal' yayin wani buki da aka yi a fadar Vatican.

Kuma a karon farko babu wani daga cikinsu da ya fito daga nahiyar Turai.

Daya daga cikin manyan malaman cocin da kaddamar yau din shi ne Archibishop na Abuja, John Onaiyekan, wanda kuma jim kadan da kaddamar da shi yace a ganinsa abu ne mai sauki a hada kai da musulmi a Najeriya wajen shawo kan manyan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Najeriya dai ta jima tana fama da fadan da ake dangantawa da addini, wanda kuma ke haddasa asarar rayuka da dama.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.