BBC navigation

An dakatar da sadarwar wayar salula a Pakistan

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:05 GMT

Tsaro a Pakistan kan Moharam

An dakatar da duk wasu harkokin sadarwa na wayoyin tafi-da-gidan ka zuwa wani dan lokaci a manyan birane da dama na kasar Pakistan don kare 'yan sunni kai hare-hare kan musulmi mabiya Shi'a.

A ranar Juma'a an yanke sadarwa a biranen Karachi da Quetta da wasu sassa na Islamabad babban birnin kasar.

'Yan shi'a na murnan ranakun Ashura da Tashura a karshen makon nan.

Hukumomin kasar suka ce, kashi casa'in cikin dari na bama-bamai ana tayar da su ne da wayoyin salula ko wayar tafi da gidan ka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.